Zargi: Shugaban NMDPRA Farouk ya yi murabus daga muƙaminsa
[ad_1]
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Murabus ɗin nasa zuwa ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu ya gayyaci Ahmed ne, bayan wasu zarge-zarge da suka shafi cin hanci da rashawa da ke da alaƙa da harkokin man fetur a Najeriya.
Tun da farko, hamshaƙin attajirin nan Aliko Dangote ne, ya zargi Farouk da amfani da ofishinsa wajen yin sama da faɗi da wasu maƙudan kuɗaɗe.
Dangote, ya miƙa ƙorafi ga hukumar ICPC a ranar Talata, inda ya zargi Farouk da cin hanci da rashawa da almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Bayan sa’o’i kaɗan da shigar da ƙorafin, ICPC ta tabbatar da karɓarsa tare da bayyana aniyarta ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar a shafukan sada zumunta na ICPC, ya ce “Hukumar ta karɓi ƙorafin Dangote a hukumance a ranar Talata 16 ga watan Disamba, 2025, ta hannun lauyansa.”
A cikin ƙorafin, “Dangote ya zargi Farouk da kashe sama da dala miliyan bakwai wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu a ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida, ba tare da bayyana sahihiyar hanyar samun kuɗin ba.”
Korafin ya ce Farouk ya yi amfani da muƙaminsa a NMDPRA wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin amfanin kansa, lamarin da ya janyo asara ga ’yan Najeriya.
A nasa martanin, shugaban hukumar NMDPRA, Ahmed Farouk, ya ce yana maraba da binciken da hukumar ICPC za ta gudanarwa a kansa.
Ya ce ya yi imanin cewa binciken zai bayar da dama a duba lamarin cikin adalci da natsuwa, tare da fayyace gaskiyar al’amura domin wanke sunansa.
Ahmed Farouk ya ƙara da cewa ba zai yi musayar zarge-zarge a bainar jama’a ba yana mai cewa zai bari binciken hukuma ya yi aikinsa yadda ya kamata.
Dangote, ya yi zargin cewa wasu hukumomin kula da harkokin mai na ƙoƙarin hana tace man fetur a cikin gida, yayin da suke barin ana ci gaba da shigo da mai daga ƙasashen waje, abin da ya ce yana nakasa tattalin arziƙin Najeriya.
Hukumar NMDPRA, wadda Farouk Ahmed ke jagoranta kafin murabus ɗinsa, na taka muhimmiyar rawa wajen kula da shigo da man fetur, farashinsa da rarrabawa a ƙasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link