Alamomin Cutar Olsa (Gyambon Ciki)

[ad_1]

Mafi yawan lokaci, ana samun ciwon Olsa ko gyambon ciki ne a wurare biyu a jikin Ɗan’adam, shi yasa masana suka kasa shi zuwa gida biyu:

1- Na cikin tumbi (Gastric ulcer)

2- Na sashen farkon ƙaramin hanji (duodenal ulcer)

  • Gwamnatin Tarayya Ta Ware  ₦42bn Don Kula Da Lafiyar ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Masu Ƙaramin Ƙarfi A 2026
  • Muhimmancin Abinci Ga Lafiya Ɗan’Adam

Alamomin Olsa:

-Na farko shi ne ciwon ciki; dukkan gyambon ciki na nuna alamu na ciwon ciki ne, wannan ciwo kuwa; yana afkuwa ne a vangaren ciki daga sama.

Haka zalika, yanayin ciwon ya fi kama da raɗaɗi irin na ƙuna ko zafi, wasu kuma su kan kamanta shi da suyar zuciya, wani lokaci kuma ana iya jin ciwon a cikin ƙirji.

Har ila yau, wannan ciwo na gyambon ciki, na da alaƙa da cin abinci, sannan alaƙar tasa da abincin abu ne mai matuƙar muhimmanci, wanda likitoci ke amfani da shi domin bambanta gyambon da ke cikin tumbi da kuma wanda ya ke a sashen farko na ƙaramin hanji.

Gyambon da ya fito a farkon hanji, ciwonsa ya fi addabar mutum da dare, haka zalika, yunwa ce ta ke tayar da wannan ciwo, amma da zarar mutum ya ci abinci, sai ciwon ya ragu ko kuma ma ya daina baki-ɗaya. A gefe guda kuma, gyambon da ya fito a cikin tumbi, akasari shi ma yunwa ce ke tayar da ciwon, amma idan ciwon ya taso yana ƙara tsananta ne a lokacin da mara lafiya ya ci abinci.

– Yawan ƙwarnafi- Wannan ma wata alama ce da ke nuna mutum na da ciwon Olsa ko gyambon ciki, sakamakon yawan jin ƙwarnafi yana taso masa.

– Haka nan, yawan gyashin magus shi ma wata alama ce ta wannan ciwo na Olsa.

– Haka zalika, idan mutum yana yawan jin ƙirjinsa na yi masa zafi, a nan ma sai ya yi maza ya garzaya don ganin likita, domin kuwa duk alama ce ta gyambon ciki.

– Yawan tashin zuciya- shi ma na ɗaya daga cikin manyan alamu na ciwon Olsa ko gyambon ciki.

Sai kuma batun yin kashin jini ko yin kashi baƙiƙƙirin, dukkannin wannan wata alama ce ta wannan ciwo na gyambon ciki, wanda aka fi sani da Olsa a turance.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *