An sake harbe wani mutum a birnin Minneapolis na Amurka

[ad_1]



Jami’an shige da fice na gwamnatin tarayya sun sake kashe wani mutum da ya fito zanga-zanga a birnin Minneapolis na Jihar Minnesota da ke Amurka.

Wannan dai shi ne mutum na biyu da aka kashe a birnin tun lokacin da gwamnatin Trump ta ƙaddamar da wani yaƙi na musammman kan ’yan cirani a jihar ta Minnesota.

Lamarin dai ya ƙara tayar da ƙura a yayin da shugabannin yankin da kuma gwamnatin tarayya ke nuna wa juna yatsa.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa jami’an tarayya sun harbe Alex Pretti, mai shekara 37, wanda ma’aikacin jinya ne a sashen ICU, yayin wata arangama da aka yi da shi.

Lamarin, wanda ya zo makonni biyu bayan harbe Renee Nicole Good da wani jami’in shige-da-fice ya yi, ya ƙara tsananta zanga-zanga tare da kiraye-kiraye da shugabannin yankin cewa jami’an tsaron gwamnatin tarayya su fice daga birnin.

Gwamnatin Trump ta ce Pretti na da niyyar cutar da jami’an tsaro, tana mai cewa an gano bindiga da harsasai a hannunsa.

Sai dai faifan bidiyo da jama’a suka ɗauka ya ayyana shakku kan bayanin hukumomin, inda aka ga Pretti yana ɗaukar bidiyo kafin a fesa masa hayaƙi, daga bisani aka kwantar da shi kasa aka harbe shi.

Bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda aka yi taho-mu-gama tsakanin jami’an tsaron kan iyaka da kuma mutumin.

Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) ta ce jami’an sun yi harbi ne domin kariyar kai bayan Pretti, wanda suka ce yana da riƙe da bindiga, ya bijire wa yunƙurinsu na ƙwace masa makamai.

Gwamnan Jihar Minnesota, Tim Walz, ya bayyana lamarin a matsayin abin firgici, yana mai cewa ba za a bar gwamnatin tarayya ta jagoranci binciken ba, illa jihar ce za ta yi hakan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi shugabannin Minneapolis da tayar da fitina, yayin da ake ci gaba da tura dubban jami’an ICE zuwa birnin domin aikin korar baƙin haure.

Lamarin ya sake harzuƙa jama’a, inda daruruwan mutane suka fito zanga-zanga duk da tsananin sanyi, suna kira da a dakatar da aikin jami’an tarayya a birnin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *