Togo ta mayar da tsohon shugaban mulkin sojin Burkina Faso gida
[ad_1]
Mahukunta sun tabbatar da cewa an kama tsohon shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Laftanar Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, a birnin Lome na ƙasar Togo, tare da mayar da shi Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso.
Ministan Shari’a na Togo, Pacome Adjourouvi, ya ce an kama Damiba ne a ranar 16 ga Janairu bisa umarnin kama shi da kuma buƙatar miƙa shi da hukumomin Burkina Faso suka aika kwanaki huɗu da suka gabata.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito Ministan na cewa an miƙa Damiba ga hukumomin Burkina Faso washegarin ranar da aka kama shi.
Damiba, wanda ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki a watan Janairun 2022, shi ma an kifar da shi bayan watanni tara a wani juyin mulki da ya ɗora Kyaftin Ibrahim Traoré kan mulki a watan Satumbar 2022.
Sai dai tun daga lokacin ne Damiba ke zaman gudun hijira a birnin Lome na Togo.
Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta sha zarginsa da shirya maƙarƙashiyar juyin mulki da yunƙurin kashe-kashe, inda ta ce yana da hannu a wani sabon yunƙurin kifar da gwamnati da aka gano a farkon wannan watan.
A cewar sanarwar gwamnatin Togo, ana tuhumar Damiba da laifuka da suka haɗa da satar dukiyar gwamnati, cin hanci da rashawa, tayar da hankula da sauransu.
Ministan Shari’ar Togo ya ce an amince da miƙa Damiba ne bayan Burkina Faso ta bayar da tabbacin kare lafiyarsa da kuma ba shi damar shari’a ta adalci.
Ya kuma jaddada cewa, duk da dawo da hukuncin kisa kan manyan laifukan cin amanar ƙasa, Burkina Faso ta tabbatar babu hukuncin kisa a shari’arsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link