Xi: A Yi Kokarin Cimma Mafari Mai Kyau Yayin Aiwatar Da Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15

[ad_1]

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jadadda cewa ya kamata a hada kai da karfi, don kokarin cimma mafari mai kyau, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a yau Talata, cikin wani muhimmin jawabi da ya gabatar, a gun bikin bude taron kara wa juna sani game da ruhin cikakken taro karo na 4, na kwamitin kolin karo na 20 na JKS, tsakanin manyan shugabanni na matsayin larduna da ma’aikata na Sin, a makarantar jam’iyya ta kwamitin kolin JKS, wato kwalejin koyon harkokin mulki ta kasa.

Shugaba Xi ya kara da cewa, gina tsarin masana’antu na zamani, da samun ci gaba baki daya a fannin tsarin masana’antu, muhimmin aiki ne a lokacin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Ya ce “Dole ne mu habaka sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko bisa halin da ake ciki, tare da inganta hadewa mai zurfi, tsakanin kirkire-kirkiren fasaha da na masana’antu. Dole ne mu ci gaba da inganta rayuwar mutane yayin da ake bunkasa tattalin arziki. Dole ne mu daidaita ci gaba da tsaro, sannan mu tabbatar da tsaron jama’a da kwanciyar hankalin zamantakewa. Dole ne mu ci gaba da daukar tsauraran matakai don kawar da cin hanci da rashawa, ba tare da tsayawa ko ja da baya ba”. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *