Ɗalibai 160 sun kammala haddar Alƙur’ani a Tsangayar Sheikh Bala Lau a Jalingo

[ad_1]



Ɗalibai 160 ne suka kammala haddar Alƙur’ani Mai Tsarki a Tsangayar Haddar Alƙur’ani ta Sheikh Bala Lau da ke birnin Jalingo na Jihar Taraba.

An gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a harabar babbar cibiyar ƙungiyar Musulunci ta Jihar Taraba a ranar Lahadin da ta gabata, inda manyan malaman addinin Musulunci daga ciki da wajen jihar suka halarta.

A jawabin da ya gabatar, Sheikh Bala Lau, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah mai hedkwata a Kaduna, ya jaddada muhimmancin bai wa matasa ilimin addini haɗi da na zamani, yana cewa hakan ne kawai zai taimaka wajen gina al’umma mai kyawawan ɗabi’u da ci gaba.

Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa haddar Alƙur’ani Mai Tsarki na da muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar Musulmi, musamman matasa, inda ya ƙara da cewa ƙungiyar Izala tana bai wa harkar ilimi muhimmanci sosai.

Ya ce ƙungiyar ta kafa tsangayoyin haddar Alƙur’ani a jihohi da dama ciki har da Kaduna, Katsina, Jigawa da wasu sassan ƙasar nan, domin bunƙasa ilimin addini da na zamani.

Sheikh Bala Lau ya kuma bayyana cewa ƙungiyar Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah tana gina babban Masallacin Juma’a a Jihar Jigawa, wanda zai taimaka wajen bunƙasa ilimin addini da na zamani.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman masu hannu da shuni, da su taimaka wajen gina makarantu domin koyar da ilimin addini da na zamani, domin inganta rayuwar matasa da makomar ƙasa.

Kazalika, ya bayyana cewa ya kafa babbar makarantar koyon sana’o’i a garin Lau, mahaifarsa, domin bai wa matasa damar dogaro da kai.

A lokacin bikin yaye ɗaliban, Babban Manajan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa, Alhaji Abubakar Dantsoho, ya bai wa kowane ɗalibi daga cikin ɗaliban 160 kyautar kuɗi Naira dubu ashirin (₦20,000) a matsayin tallafi da ƙarfafawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *