Kamfanonin Sin Sun Gudanar Da Taron Bayar Da Tallafi A Masar
[ad_1]
Kungiyar ‘yan kasuwan kasar Sin da ke Masar da kungiyar Orman ta Masar sun gudanar da wani taron ba da tallafi cikin hadin gwiwa a jihar Giza jiya Litinin, don taimaka wa iyalai mabukata a kasar ta Masar.
A cewar Zhang Yaqiang, babban jami’i kuma mataimakin jakada a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Masar, gangamin tallafin da aka yi na bana ya samar da kudin Masar fam miliyan 3, kwatankwacin dalar Amurka 56,800, don tallafa wa iyalai mabukata a kasar, kana daga fara shirya taron zuwa yanzu, an taimaka wa dubun dubatan iyalai a fadin kasar..
Taron ba da tallafin ya zama wani muhimmin dandali na sada zumunci, da tuntubar juna, da kuma hadin gwiwa tsakanin Sin da Masar, kamar yadda Zhang ya bayyana. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link