Da dumidumi-  Barayin Daji Sun Auka wa Jikamshi Da Maraicen Nan

[ad_1]



Da dumidumi-  Barayin Daji Sun Auka wa Jikamshi Da Maraicen Yau

Yanzu haka Barayin Daji na cin karensu ba babbaka a garin Jikamshi hedikwatar Karamar Hukumar Jikamshi ta Jihar Katsina.

Wata majiya mai tushe daga garin na Jikamshi ta tabbatar da cewa, Barayin da suka shigo garin tun wajen karfe 6 na yamma dauke da muggan makamai har ya zuwa yanzu suna cikin garin suna harbin duk wanda suka ci karo da shi a waje.

Majiyar ta tabbatar da cewa, sun harbi mutane da dama wadanda kuma aka kasa kai su asibiti saboda kowa gudun ransa.

Labarin da ya sa kowa ya koma cikin gida ya boye. Wanda ta kai har ya zuwa yanzu da yawan mutanen garin basu yi buda bakin azumin da ke a bakinsu ba.

Majiyar ta tabbatar da cewa, har ya zuwa yanzu dai babu alamun wani dauki daga hukumomin tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *