An ɗage shari’ar El-Rufai da DSS zuwa watan Afrilu

[ad_1]



An sake ɗage shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, bayan da aka kasa gabatar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar wannan Larabar.

Ya bayyana cewa lauyan mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu ta ba da wa’adin makonni biyu domin a bai wa jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) damar gabatar da El-Rufai, wanda a yanzu haka yake hannun Hukumar Yaƙi da Rashawa ICPC.

Sai dai lauyan El-Rufai, Wole Iyamu, ya shaida wa kotu cewa babu wani dalili da zai sa a ce ba za a iya gabatar da wanda yake hannun wata hukuma ta gwamnati ba, wanda a cewarsa, “ai duk gwamnati ɗaya ce, don haka ba sai an nemi ƙarin lokaci ba.”

Daga bisani, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da ɗage shari’ar har zuwa watan Afrilu, abin da a cewar Muyiwa ya zarce wa’adin da lauyoyin suka nema tun farko.

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai na tsare tun ranar 16 ga Fabrairu, bayan ya kai kansa hedikwatar EFCC domin amsa gayyatar da ta yi masa.

Daga bisani kuma aka ce ICPC ta karɓe shi a daren 18 ga watan, kuma har kawo yanzu ba a ba da belinsa ba.

A gefe guda kuma, ana sauraron ƙarar da El-Rufai ya shigar a gaban kotu kan DSS, yana zargin take masa wasu haƙƙoƙinsa da dokokin Kundin Tsarin Mulki suka tanada.

Lamarin dai na ci gaba da ɗaukar hankali, musamman ganin yadda batun ya shiga tsakanin hukumomin tsaro daban-daban.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *