Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata
[ad_1]
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida.
Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri.
A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu.
Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta tabbatar da wannan shiri.
Kakakin Majalisar, ya yaba da ƙoƙarin Uwargidan Gwamnan, inda ya ce wannan ziyarar “ta tarihi ce” kuma ya tabbatar da goyon bayan majalisar wajen ganin an aiwatar da ƙudirin.
Haka kuma, wakiliyar Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Miss Omowumi Gbamis, ta ce wannan doka zai taimaka wa mata su ci gaba da aiki lafiya tare da inganta lafiyar jarirai.
Kodinetan CS-SUNN a Gombe, Misis Comfort Mukollo, ta bayyana cewa suna aiki tare da UNICEF da ma’aikatun gwamnati don tallafa wa shirye-shiryen kula da abincin uwa da jariri tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin shayar da nono.
Daga cikin manyan jami’an da suka nuna goyon baya akwai Kwamishiniyar Harkokin Mata, Asma’u Mohammed Iganus, da Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar, Siddi Buba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link