Ana Zargin NFF Da Shigar Da Ƙarar Bogi A Kan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo
[ad_1]
Shugaban wata ƙungiya da ke neman a gyara harkar ƙwallon ƙafa a Nijeriya, Prince Harrison Jalla, ya ce NFF ta kai ƙarar ƙarya ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA).
Ya ce sun zargi ƙasar Congo da amfani da wasu ‘yan wasa da ke da katin zama ‘yan ƙasa biyu, bayan Nijeriya ta kasa samun gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
- Yadda Jigo A APC Na Kano Ya Rasu A Otal A Abuja
- 2027: Tinubu Na Son A Naɗa Shi Sarauta Ne, Ba Zaɓe Ba — Dino Melaye
A wata sanarwa da ya fitar, Jalla ya ce NFF ta shigar da wannan ƙorafi ne ba tare da gaskiya ba.
Ya kuma ce hakan wata dabara ce domin a kau da hankalin ‘yan Nijeriya daga gazawar da hukumar ta yi.
Ya ƙara da cewa akwai matsalar shugabanci a cikin NFF, ciki har da zargin cin hanci da rashawa.
Jalla ya kuma ce an aike da ƙorafi, wanda a cewarsa hakan na nuna cewa an shirya shi ne domin yaudarar jama’a.
Ya buƙaci NFF ta fito ta bayyana cikakken bayani kan ƙarar da ta shigar da kuma amsar da FIFA ta ba su.
[ad_2]
Source link