NSCDC ta tura jami’ai don tabbatar da tsaro a Gombe
[ad_1]
Rundunar Tsaron farin kaya ta Sibil Difense NSCDC a Jihar Gombe, ta tura jami’ai 726 zuwa muhimman wurare a faɗin jihar domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin bukukuwan Easter.
Kwamandan rundunar a jihar, Jibrin Idris ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon da ya fitar mai ɗauke da sanya hannun jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar CSC Buhari Sa’ad, sa’oi kaɗan gabanin bukukuwan.
Saƙon cikon umarni ne na Babban Kwamandan NSCDC na ƙasa, Dokta Ahmed Abubakar Audi, wanda ya umarci dukkanin rassan jihohi su ƙara ƙaimi wajen tsaro a lokacin bukukuwa.
Ya ce, an zaɓo jami’an ne daga sassa daban-daban da kuma rundunoni na musamman, tare da tura su wuraren ibada, wuraren shaƙatawa, tashoshin mota, kasuwanni, manyan hanyoyi da sauran wuraren taruwar jama’a.
Kwamandan ya ƙara da cewa, jami’an rundunoni na musamman kamar na yaƙi da ta’addanci (CTU), Agro Rangers, rundunar yaƙi da yin ɓarna, sashen kula da ibtila’o’i, sashen leƙen asiri da kuma rundunar mata masu ɗauke da makamai, duk an tanade su domin gudanar da wannan aiki yadda ya kamata.
Haka kuma ya bayyana cewa wannan shiri ya haɗa da kare muhimman kadarorin ƙasa da ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, ruwan sha, layin dogo, hasumiyoyin sadarwa da bututun mai, domin hana lalata su a lokacin bukukuwan.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar na shirye ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a duk tsawon lokacin bukukuwan.
Ya kuma gargaɗi jami’an da aka tura da su kasance masu ƙwarewa, ladabi da jajircewa yayin gudanar da aikinsu, tare da mutunta haƙƙoƙin ɗan Adam.
Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar Easter, ya buƙace su da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar Gombe da ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma shawarci jama’a da su kasance masu lura da harkokin tsaro, su guji cunkoso, tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani abu ko motsi da suke zargi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link