Jimillar Tashoshin 5G Na Sin Ta Kai Miliyan 4.83
Ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin, ta ce a cikin watanni 11 na farkon wannan shekara, harkar sadarwa ta Sin ta ci gaba da gudana cikin kwanciyar hankali. Hukumar ta ce ya zuwa karshen watan Nuwamban bana, jimillar tashoshin 5G a kasar ta kai miliyan 4.83, wato ya karu da dubu 579, idan aka kwatanta da na karshen shekarar da ta gabata.
Bayanan sun nuna cewa, a cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, kudaden shiga na ayyukan sadarwa sun kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.6096, wanda ya karu da kashi 0.9% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Kazalika, yawan masu amfani da fasahar 5G ya ci gaba da karuwa, inda zuwa karshen watan Nuwamba, jimillar masu amfani da wayar hannu na manyan kamfanonin sadarwa 3, da na gidan talabijin na Sin ya kai biliyan 1.828, wanda ya karu da miliyan 38.54 idan aka kwatanta da na karshen shekarar da ta gabata. (Amina Xu)