Cin zarafin Kansila ya jefa hadiman gwamna a matsala a Gombe
[ad_1]
’Yan uwan Kansilan Mazabar Unguwar Shamaki a Gombe, Abdurrahman Abubakar Dan Buba, sun roƙi Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, da ya ɗauki matakin gaggawa kan wasu hadimansa biyar da ake zargin sun ci mutunci da kaskantar da zababben wakilin jama’a.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, ’yan uwan kansilan sun bayyana cewa mutanen da ake zargi dukkansu na rike da mukamai a gwamnatin jihar, abin da suka ce na iya jefa gwamnati cikin badakala da tayar da hankalin jama’a.
Wani dan uwan Kansilan mai suna Abu Safyan, ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda aka ga direban Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, a cikin bidiyo yana cin zarafi tare da dukan kansilan.
Lamarin ya bazu a kafafen sada zumunta da manyan kafafen yada labarai na ƙasa, inda ya jawo ce-ce-ku-ce da damuwa daga al’umma.
Ya ce ba za su lamunci yadda aka ci zarafin ɗan uwansu ba, don haka suke kira ga gwamna da ya ɗauki mataki domin hana irin wannan aukuwar nan gaba.
’Yan uwan kansilan, ciki har da mahaifinsa, sun yi kira ga gwamna da ya umarci gudanar da bincike mai zurfi tare da ɗaukar mataki bisa doka, domin kare mutuncin zababbun wakilan jama’a da martabar gwamnati.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da:
- Alin Baban Kaya, SSA kan Harkokin Hulɗa da Jama’a
- Rabiu B. Goro, SSA kan Kafafen Sada Zumunta
- Muttaka Sharubutu, SSA kan Kafafen Sada Zumunta
- Garba Muhammad (Mai Rago), SSA kan Harkokin Siyasa
- Adamu Danko, SSA kan Harkokin Cikin Gida
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link