Ɓangaren Ilimi Ya Samu Rinjaye A Kasafin ₦985.9bn Na 2026 Da Gwamna Sani Ya Sanya Wa Hannu
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira biliyan 985.9, inda ɓangaren ilimi ya sami mafi girman kaso na kashi 25 cikin 100 na jimillar kasafin kuɗin.
Gwamnan ya rattaba hannun ne a ranar Litinin a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna, inda ya bayyana shirin kasafin a matsayin wani abu da ke nuna jajircewar gwamnatinsa na amfani da nasarorin da aka samu tare da shimfiɗa harsashi mai ƙarfi don samar ci gaba mai ɗorewa.
A cewar Sani, kasafin kuɗin shekarar 2026, ya fi mayar da hankali kan zuba jari da nufin hanzarta ci gaba a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa, Naira biliyan 698.9, wanda ke wakiltar kashi 70.9 cikin 100 na jimillar kasafin kuɗin, an ware shi ne don zuba jari don bunƙasa ababen more rayuwa, faɗaɗa tattalin arziki da inganta samar da ayyuka na gari.
[ad_2]
Source link