Kwakwazon Da Amurka Ke Yi Da Batun Wai “Dakile Makaman Nukiliyar Kasar Sin” Munakisa Ce Da Ta Saba Yi
[ad_1]
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi nuni da cewa, kwakwazon da kasar Amurka ke yi da batun wai “dakile makaman nukiliyar kasar Sin” ba komai ba ne illa munakisar da ta saba yi, da nufin samar da hujjar da za ta hanzarta sabunta karfin makamanta na nukiliya da kuma kawo cikas ga tsarin zaman lumanar duniya.
Lin Jian ya ce, Amurka, a matsayinta na kasa mai karfin makaman nukiliya da ke zaune a saman babban rumbun nukiliya mafi girma a duniya, dole ne ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na musamman da kuma babban hakkin da ke kanta na kwance damarar makaman nukiliya, da kara himmar rage yawan makaman rumbunta na nukiliya, da samar da yanayi ga sauran kasashe da suka mallaki makaman nukiliya su shiga cikin shirin kawar da makaman nukiliya. Wannan ne ya kamata ya zama babban abin da Amurka ke bai wa fifiko.
Lin Jian kuma ya yi nuni da cewa, kasar Sin na ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar kin fara amfani da makaman nukiliya da kuma amfani da dabarun nukiliya dake mai da hankali kan kare kai. Kasar Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya daidai gwargwadon abin da take bukata na tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar tara makaman nukiliya da kowace kasa. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen bitar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya da kuma tarukan kasashen P5 (watau kasashe biyar masu karfin makaman nukiliya), kuma tana ci gaba da tattaunawa da bangarori daban-daban kan batun kawar da makaman nukiliya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link