Lambobin NIN Da CAC Za Su Zama Lambobin Biyan Haraji Daga 2026— FIRS


Lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ta bayar, ta zama lambar biyan harajin da gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro wa ‘yan Nijeriya wanda za a fara daga Janairun 2026, a cewar Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya (FIRS).

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya da ke da asusun banki ke tambayar yadda za su mallaki lambar biyan haraji (TIN).

  • Jimillar Tashoshin 5G Na Sin Ta Kai Miliyan 4.83
  • An Bullo Da Sabon Daftarin Dokar Kiyaye Muhallin Halittu Na Kasar Sin

A cewar bayanai da NIMC ta fitar, jimillar ‘yan Nijeriya miliyan 123.9 ne suka mallaki (NIN) ya zuwa Oktoban 2025.

A wata sanarwa ta wayar da kan jama’a game da sabbin dokokin haraji da aka fitar a shafin X a ranar Litinin, Hukumar ta fayyace cewa, ga masu kamfanoni, lambar RC da Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC) ta bayar, itace lambar shaidar biyan harajinsu a ƙarƙashin sabon tsarin haraji.

Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya (NTAA) da ke shirin fara aiki daga Janairun 2026, ta wajabta cewa, dole ɗaiɗaikun ‘yan Nijeriya da kamfanoni su mallaki lambar haraji.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *