Bahallatsar Gabas Ta Tsakiya: Sin Da Pakistan Sun Ba Da Mafita

[ad_1]

Fitinar da aka tayar a yankin Gabas ta Tsakiya ta addabi duniya, kuma babu abin da ake nema face mafita mai adalci da za ta kai ga samun dauwamammen zaman lafiya. Wannan ya sa kasar Sin da Pakistan suka gabatar da wata sahihiyar shawara da za ta zamo mafita ba kawai ga dakatar da yake-yake ba har ma da samun zaman lafiya mai dorewa a yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya baki daya. Kowanne daga matakai biyar da shawarar ta kunsa, idan aka aiwatar da shi yadda ya dace, akwai yakinin zai karfafa dawo da kwanciyar hankali, saboda yana dauke da darussa daga tarihi wajen warware rikice-rikice da samar da zaman lafiya.

Mataki na farko shi ne dakatar da barin wuta nan da nan wanda yake nuni da kafa tubali na bin hanyar diflomasiyya. Tsagaita wuta na samar da yanayi mai kyau domin tattaunawa, da isar da kayan agaji, da kuma gina amincewa tsakanin bangarori masu dauki-ba-dadi. A tarihi, ana iya ganin tasirin haka a yakin Larabawa da Isra’ila a shekarar 1973, inda tsagaita wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta ya kawo karshen fada, ya kuma bude kofa ga yarjejeniyoyin sulhu.

Mataki na biyu shi ne fara tattaunawar sulhu da wuri-wuri wanda yake nuna cewa, amfani da karfin soji ba zai taba ba da mafita ba. Tattaunawa ita ce hanya mafi inganci wajen magance silar rikici, da warware sabani, da kuma samar da mafitar da kowa zai amince da ita. Yarjejeniyar Dayton ta 1995, wadda ta kawo karshen yakin Bosnia, daya ce daga misalan alfanun tattaunawa da wuri-wuri.

Kazalika, daga matakan da shawarar ta gabatar, kiyaye barnata wuraren da ba na soja ba shi ne mataki na uku. Wannan yana da matukar muhimmanci, domin tabbatar da tsaron wuraren fararen hula kamar asibitoci, makarantu, da gidaje wajibi ne a karkashin dokokin kasa da kasa. Yarjejeniyoyin Geneva sun dade suna jaddada dokokin kare fararen hula, kuma aiwatar da su suna taimakawa sosai wajen rage asarar rayuka da dukiyoyin fararen hula.

Mataki na hudu shi ne kiyaye tsaron hanyoyin sufurin jiragen ruwa wanda tabbas ko makaho ya shafa, ya san wannan yana da matukar tasiri ba ga yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya ba har ma ga duniya baki daya. Rufe mashigin Hormuz ya haifar da babbar tangarda ga zirga-zirgar jiragen ruwa musamman na dakon makamashi zuwa sassan duniya, don haka samar da wani hadin gwiwa mai adalci a bangaren sintiri zai taimaka ga samun zaman lafiya da habaka tattalin arziki.

Mataki na biyar da shawarar ta Sin da Pakistan ta gabatar shi ne girmama kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya wanda rashin yin hakan ne ya sa Amurka da Isra’ila suka yi gaban kansu wajen kaddamar da hari kan Iran, inda lamarin ya haifar da masifar da ake ciki a yankin. Kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya ya haramta keta ’yancin wata kasa, da yin katsalandan daga waje da kuma jaddada warware rikici ta hanyar zaman lafiya. Wannan ne yake ba kasashe damar magance matsaloli cikin adalci.

Hakika, duk da ana fuskantar kalubale musamman daga kasashe masu kunnen kashi, wannan shawara mai matakai biyar da Sin da Pakistan suka gabatar, mafita ce ga samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *