Me Ya Sa Kungiyar Tattara Bayanai Ta Kasa Da Kasa Ta Samu Mazauni A Birnin Beijing?

[ad_1]

Kungiyar tattara bayanai ta duniya (WDO) ta kafu a nan birnin Beijing a ranar 30 ga wata, lamarin da ya jawo hankalin duniya sosai. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar kafuwar kungiyar WDO. An kafa kungiyar bisa shawara da taimakon Sin, kuma hedkwatarta ta samu mazauni a birnin Beijing, matakin da bayyana cewa, Sin ta sauke nauyin dake wuyanta a matsayin babbar kasa mai karfin bayanai a duniya.

Zaman kungiyar a birnin Beijing, ba kawai nuna amincewa da ci gaban bayanai da sarrafa bayanai na Sin ya yi ba, har ma da biyan bukatu da tsamanin al’ummar duniya. Yayin bikin kafa kungiyar, Sin ta gabatar da shawarwari 3 game da bude kofa da samun ci gaba da tsaro, wadanda suka jawo hankalin kasa da kasa. Jack Perry, shugaban kawancen “The 48 Group Club” da ya kasance mambar kungiyar WDO, ya ce, bayanai ba su da shinge, kuma Sin tana yin iyakacin kokarinta don neman hanyoyin amfanar da kowa da kowa bisa sakamakon ci gaban tattalin arzikin dijital.

A cikin ‘yan shekarun nan, Sin ta dade tana kokarin binciken hanyoyin inganta sarrafa bayanai na duniya gwargwadon karfinta. Kuma a nan gaba, Sin za ta kara taka rawar gani wajen karfafa boyayyen karfin bayanai da inganta sarrafa su.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *