‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace 11 a Sakkwato

[ad_1]



‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da sace wasu mutum 11, sannan sun raunata mutum biyu a garin Malamawar Yari da ke Ƙaramar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato.

‘Yan bindigar sun kai wa garin hari ne da misalin ƙarfe 11:40 na ranar Talata, inda suka sace mata takwas, da maza uku, da ƙaramin yaro.

Mazauna garin sun bayyana cewa mutum bakwai daga ciki ‘yan gida ɗaya ne, sai kuma mata bibbiyu daga gidaje guda biyu.

“Sun shigo ƙauyenmu ta hanyar da ta haɗa mu da ƙaramar hukumar Rabah. Suna shigowa suka hau harbi kan mai uwa da wabi, in da suka kashe mutum biyu.

“Sai wasu mutum biyu da suka samu raunuka, da kuma mutum 11 da suka sace.” in ji wani da lamarin ya faru a kan idonsa.

Waɗanda suka samu raunukan na kwance a asibiti inda suke karɓar magani.

Wasu daga cikin mazauna garin sun koka kan halin rashin tsaron da suje ciki, wanda hakan ke janyo yawan kai musu hari daga ‘yan ta’adda.

Ɗaya daga cikin mazauna garin ya ce ko a watan da ya gabata, ‘yan bindigar sun kawo musu hari, inda suka kashe mutum guda, suka kuma sace mutane da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Ahmad Rufai ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce bai tantance adadin mutanen da aka sace ba tukuna, sai ya samu cikakken bayani daga shugaban ofishin ‘yan sandan ƙaramar hukumar Kware.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *