Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Fetur, Ta Dakatar Da Lodi
[ad_1]
Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur da N101, inda ta ɗaga farashin N774 zuwa N875 kan kowace lita, tare da dakatar da lodin fetur sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Wani babban jami’i a matatar ya tabbatar da cewa an yi bitar ne saboda sauye-sauyen da ake samu a farashin ɗanyen mai na duniya da kuma kuɗin sake dayo kaya. Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen mai ya haura dala $80 kan kowace ganga, lamarin da ya sa aka dakatar da lodin fetur da tsakar daren 2 ga Maris, 2026.
- Kamfanin Kayan Ɗanɗanon Kayan Miya Na Dangote Ya Gwangwaje Abokan Cinikayyarsa 50 Da Kyaututtukan Motoci
- Matatar Dangote Na Da Ƙarfin Samar Da Mai Fiye Da Buƙatar Nijeriya
An bayyana cewa dakatarwar ta shafi fetur kaɗai, yayin da lodin man dizal (AGO) ke ci gaba. Haka kuma, an dakatar da fitar da sabbin takardun izinin sayen kaya, wanda ya haifar da tsaiko a sabbin mu’amalolin kasuwanci.
Matakin ya jawo martani a ɓangaren kasuwancin man fetur, inda wasu ƴan kasuwa masu zaman kansu suka dakatar da sayar da Fetur, suna masu cewa kasuwa ta riga ta fara la’akari da haɗarin hauhawar farashi, kuma babu wanda ke son sayarwa ƙasa da kuɗin sake sayen kaya.
Masana makamashi sun yi gargaɗin cewa idan farashin ɗanyen mai ya kai sama da dala $90 kan ganga, ana iya ganin ƙarin farashi a fetur da dizal, musamman idan rikice-rikicen da ke tsakanin Amurka da Iran suka ƙara dagulewa harkar kasuwancin makamashi a duniya.
[ad_2]
Source link