Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi
…. ci gaba daga makon da ya gabata.
A bangaren kyawawan dabi’un da muka zayyanu, Annabi SAW, ma’aiki ne ga duk halitta.
2. Annabi Muhammad SAW rahama ne ga halitta (wama arsalnaka illa rahmatan lil’alamin). Ana nufin Annabin, sauki, tausayi, jinkai ga duk halitta, don haka, duk wani abu mai tsanani ba na Annabi ba ne, SAW. Duk wanda ya bi Annabi SAW, shi ake kira Mumini da fadin Ubangiji, “ya ayyuhannabiyyu hasbukallahu wa manittaba’aka minal mu’uminin”, amma ga halitta baki daya, Annabi SAW na duk halitta ne a kyawawan dabi’u.
Shari’ar Annabi SAW, “Hanafiyya” ce ta kakansa Annabi Ibrahim (AS), ma’ana abu mai karkacewa, amma kuma babu shakka Addinin Annabi SAW “Mustakimi” ne. To ta yaya shari’arsa ta zama HANAFIYYA? Ana nufin karatun daya ne amma yana sassauyawa da sauyin zamani/halitta. Alkur’ani da muke amfani da shi a yanzu, shi ne wanda Annabi SAW ya yi amfani da shi a iya zamanin sa, a iya al’ummar da ke wancan lokacin kuma shi ne za a ci gaba da amfani da shi har karshen zamani. A kowane Tafsirin Alkur’ani na Malaman da suka gabata, sai ka samu wayewa ta irin zamanin wanda ya rubuta Tafsirin, amma abin da ya same mu Musulman wannan zamanin, so muke dole sai mun koma wayewa irin ta zamanin Annabi SAW, dole sai an fassara Alkur’ani da irin yadda sahabbai (RA) suka yi, sun yi iya na zamanin su ne. In mun tafi a hakan, kamar ba mu yarda Shari’ar Annabi SAW Hanafiyya ba ce. Mu kalli mutanen Aljannah, duk lokacin da aka kawo musu abinci, sai su ce, “Kalu hazallazi ruzikna min kabli, wa’utu bihi mutashabiha – ba wannan shi ne abincin da muke ci a duniya ba, sai a ce ku taba ku ji, sai suga bambanci”, iri daya, amma akwai bambanci na irin zamani da wuri. Da haka, za mu gane, karatun iri daya amma duk lokacin da ilimi ya karu, karatun ma sai ya karu.
Misali, a baya babu Glass na ido amma a yanzu muna amfani da glass, don karfafa ganin ido. Akwai kuma glass na binciken kwayoyin halitta (microscope), shi kuma karfin shi ya dara glass na ido, sannan kuma akwai na NASA wanda ake amfani da shi wurin hangen duniyar wata. Da wannan za mu fahimta, addini daya, karatu daya amma mai canzawa. Ya dace, mu rika kallon Alkur’ani cewa, na kowane zamani ne ba daya kadai ba, malamai kuma su kalle shi da irin fahimtar wannan zamani, in ba haka ba, komai ya watse mana, ba mu da kimiyyar zamani an barmu da Akida – ita ma har yanzu ba mu cimmata ba, an barmu da buge-buge da kashe-kashe, kullum sai dai mu ce, kayan Kafirai ne, mu kuma ba mu da na mu.
A wannan bangaren, cewa, shari’ar Annabi SAW mai canzawa ce da sauyawar zamani, Annabi SAW, RAHAMA ne ga duk halitta.
Shari’ar Annabi SAW, “Hududu – iyaka” ce . Misali, Haddin kisa – wanda ya kashe a kashe shi, ba dole sai wannan hukuncin ba. Duk duniya tana amfani da wadannan abubuwan guda Uku a hukunci: Biyan fansa, Kurkuku, ko zartar da lamari. Shari’ar Annabi tana da iyaka – a wani wuri, Ubangiji ya kan fadi karshen mataki amma, a iya saukowa, kamar hukuncin kisa, a iya saukowa zuwa ga fansa, kurkuku ko yafiya. A wani wuri kuma, ya kan fadi farkon mataki, a iya karawa, kamar nisabin zakka, ka iya kara abin da ka ga dama.
A kan haka, za mu iya cewa, kowacce Kasa akan shari’ar Musulunci take, saboda akwai wani mataki da ta dauka da ke cikin iyaka.
Manzon Allah SAW, rahama ne ga halitta baki daya, mu ne muka mayar da shari’arsa Azaba ga halitta saboda irin Fikhun da aka kakkafa. Don haka, akwai abubuwan da ya dace duk a zubar da su. Ko dai mu zubar da su da kanmu ko mu zubar da su dole. Don a yau, akwai abin da kana zaton addini ne, in ka aikata shi, Musulmin ne ‘yan uwanka za su kama ka su mika ka ga duniya, su ce kai dan ta’adda ne. Sabida da yawan wasu karatuttukan, Daular Abbasawa ce ta kafa su, sabida wani abu daban.
3. Annabi Muhammad SAW cika makon Annabawa ne. Annabi SAW ya cika Manzonci (Risala). Me sauran Annabawa suka yi kira akai? Sun zo da kira zuwa ga Allah da tausayin dan Adam.
Annabi Nuhu (AS), ya yi kira zuwa ga Allah da girmama iyaye, “wa’abudullaha wala tushriku bihi shai’an, malakum min ilahin gairuhu, afala tattakun”, “rabbigfirli wali walidayya waliman dakala baitiya mu’uminan…”
Wasayar Ashri (10), itace Furkan a wurin Annabi SAW, itace Hikima a wurin Annabi Isa (AS), kuma wasayal Ashri a wurin Annabi Musa (AS). A nan ne za mu fahimci ma’anar Hadisin “Bu’istu li’utimmima makarimal aklak – an turo ni don in cika kyawawan dabi’u”. Wannan ya nuna, sauran Annabawa sun zo da kyawawan dabi’u amma Annabi SAW, ya zo don ya cika su. Wadannan wasayal Ashri (10) da suratul An’am ta zo da su tun daga ayar “Kul ta’alau atlu ma harrama rabbukum alaikum, alla tushriku bihi shai’an, wa bil walidain ihsana…” har zuwa “wa’anna haza siradi mustakiman fattabi’uhu”, da sauran Annabawa suka zo da su, Ubangiji tabaraka wata’ala ya kara wa Annabi SAW kusan Ashirin (20), inda na shi suka kai Talatin (30-31).
Mun zayyano wasayal Ashri (10) a karatun farko na makon da ya gabata, yanzu za mu dora daga na 11:
11- An haramta muku auren uwayenku mata, da ‘ya’yanku mata, da ‘yan uwanku mata, da ‘yar uwar mahaifinku, da ‘yar uwar mahaifiyarku, da ‘ya’yan ‘yan uwanku mata, da ‘ya’yan ‘yan uwanku maza, da uwayenku da suka shayar da ku nono, da ‘yan uwanku da kuka sha nono tare, da agololinku da kuka raina a gidanku, da matayen ‘ya’yanku, kuma karku hada ‘yan uwa biyu.
Har ila yau, an haramta muku auren kowace mace da take katangaggiya (wacce take da wanda yake kula da ita ba miji ba, sai kun nemi izini daga wannan da ke kula da ita, in babu sai hukuma ta yi), ko kuma a yi kwantiragin auren – magana ce mai fadi.
Banda wannan abun da muka lissafo, komai an halasta muku amma sai kun nema da kudinku sannan ku aura ko kuma ku yi kwantiragi, kuma ku kare kanku daga taruwa akan saduwa da mace daya ko matan su taru akan namiji daya.
Akwai haram a bangaren abinci, ga su kamar haka: An haramta muku mushe, da jinin da ya zuba, da naman Alade, da dabbar da aka yanka ba da sunan Allah ba, da dabbar da aka shake har ta mutu, da dabbar da aka buga a kai ta mutu, da wadda ta fado da sama ta mutu, da wacce ‘yar uwarta ta soka da kaho ta mutu, da wadda namun daji suka ci wani sashinta har ta mutu, da dabbar da aka yanka wa wani mutum-mutumi ko wani jarumi da sunan bauta ba wacce aka yanka a liyafar bikin tunawa da wasu jarumai ba, wannan halal ne. Amma duk wanda ya matsu, ba laifi zai iya cin duk wannan abincin da muka lissafo.
Bugu da kari, Allah ya haramta muku riba, sannan mafi hadari, yi wa Allah karya “wa antakulu alallahi mala ta’alamun.”
Riba, ana nufin ajiye wasu kudade da nufin bayarwa rance, amma za a dawo da fiye da abun da aka karba rancen. Amma wasu taron jama’a masana kasuwanci ko wani kamfani da zai amsa kudaden jama’a domin yin kasuwanci sannan a raba ribar da aka samu, wannan kasuwanci ne na “Halal” ba “Riba ba”.
Alhamdulillah, wannan Haram-haram da muka lissafo, babu wata Majalisar Dokoki a duniya da za ta halasta su.