Za A Gudanar Da Bikin Ajiye Furanni Don Jinjinawa Jarumai A Ranar 30 Ga Satumba
[ad_1]
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar.
A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasar, tare da wakilai daga sassa daban-daban, za su ajiye furanni don jinjinawa jarumai da suka sadaukar da rayukansu saboda kasa a filin Tian’anmen. A lokacin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG zai watsa wannan biki kai tsaye.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link