Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Titi Mai Tsawon Kilomita 35 Da Ya Haɗa Al’ummomi 76 A Kaduna

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a ranar Litinin ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 35 da ya haɗa Ƙananan Hukumomin Igabi, Kajuru Da Chikun, wanda aka bayyana a matsayin aikin hanya mafi tsayi da aka yi a jihar Kaduna cikin shekaru 20 da suka gabata.

Titin, wanda ya haɗa Gadar Gayan ta hanyar Gwaraji zuwa mahaɗar Kujama, an gina sabuwar gadar Kogin Kaduna mai tsawon mita 130 akan titin wanda ya haɗa al’ummomi sama da 76 manoma. Hakan zai haɓaka tattalin arzikin Ƙauyukan yankin.

Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Sani ya bayyana aikin a matsayin tarihi na cigaban samar da abubuwan more rayuwa na Jihar Kaduna.

Ya tuna cewa, an ƙaddamar da aikin gina titin ne a watan Janairun 2024 tare da alƙawarin samar da hanyar sufuri mai Inganci, kuma yau ga shi an cika wannan alƙawarin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *