Iran ta kama wani mutum kan zargin yi wa Amurka da Isra’ila leƙen asiri
[ad_1]
Ma’aikatar tattara bayanan sirri ta Iran ta sanar da kama mutane 30 da ake zargi da aikata leƙen asiri, ciki har da wani baƙo ɗan ƙasar waje, a rana ta 11 da fara yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Ma’aikatar ta ce cikin waɗanda aka kama akwai wani ɗan ƙasar waje da ake zargi da tura muhimman bayanan tsaro ga wasu gwamnatocin ƙasashen yankin Tekun Fasha guda biyu, waɗanda daga bisani suka miƙa bayanan ga Amurka da Isra’ila.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin Mizan Online na ma’aikatar shari’a, hukumomin Iran sun ce an kama baƙon mutumin ne a arewa maso gabashin ƙasar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ƙasar da mutumin ya fito ba, kuma ba ta fayyace ranar da aka kama shi ba.
Kazalika, sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu mutane 19 daga cikin waɗanda aka kama ana zargin su da zama ma’aikatan jarida da kuma masu hulɗa da masu adawa da gwamnati da ke da alaƙa da Isra’ila.
Hukumomin Iran ba su bayyana ƙasashen da ake zargin suna da hannu a lamarin ba, haka kuma ba su bayar da cikakken bayani kan sauran waɗanda aka kama ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link