Neymar Ya Fi Messi, Ronaldo Da Mbappe Hazaka A Kwallon Kafa – Cafu
[ad_1]
Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil Cafu ya bayyana cewa dan wasan gaban kasar Brazil Neymar yana da baiwar iya kwallo fiye da manyan yan wasa kamar Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, da Kylian Mbappe, inda y kara da cewa dole ne mahukuntan babbar tawagar kwallon kafa ta kasar Brazil su sanya sunan tsohon dan wasan na Barcelona da PSG a cikin jerin yan wasan da zasu wakilci kasar a babbar gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026.
Cafu wanda ya lashe gasar cin kofin Duniya sau biyu ya yi imanin cewar Neymar nada gudunmawar da zai bayar a gasar ta bana, inda yace duk da cewar Ronaldo da Messi sun taka matsayin da Neymar din bai taka ba a harkar kwallon kafa amma dolene a sanya sunansa cikin jerin yan wasanda keda baiwa a harkar kwallon kafa a Duniya.
“A ganina, Neymar ya fi Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, da Kylian Mbappe.” inji Cafu, wanda ya jaddada cewa dole ne Brazil ta koyi darasi daga nasarar Argentina ta hanyar gina tawagar kasar a bayan Messi wanda ya kwatanta kwarewarsa da Neymar, yana mai cewa dan wasan ya shafe shekaru yana daukar nauyi mai yawa ba tare da irin goyon bayan da tsoffin taurarin Brazil suka samu ba.
“Lokacin da Argentina ta buga wa Lionel Messi wasa, sun lashe kofuna, hakazalika a shekarar 2002, mun buga wa Ronaldo da Rivaldo wasa, yayin da kuma muka taimaka wa Ronaldinho,” inji Cafu”, amma kuma Neymar yana iyakar kokarinsa ba tareda wannan goyon baya ba, tsawon shekaru 15 yana daukar nauyin shi kadai, amma kuma yanzu akwai yan wasa a kusa da shi wadanda za su iya taimaka masa domin ya cimma burinsa na kwallon kafa a matakin kasa Cafu ya kara da cewa.
[ad_2]
Source link