Ana fargabar mutane sun rasu bayan rami ya rufta kansu a Kano

[ad_1]



Ana fargabar ma’aikata da dama sun mutu bayan wani ramin ƙasa ya rufta a kansu a ƙauyen Ridawa da ke Ƙaramar Hukumar Ghari a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, lokacin da ma’aikata ke haƙar ƙasa a cikin wani rami mai zurfi.

Ramin ya rufta ba zato ba tsammani, inda ya danne mutane da dama.

Shaidu sun ce lamarin ya jawo tashin hankali a yankin, inda sauran ma’aikata da mazauna yankin suka garzaya wajen domin fara aikin ceto.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ghari/Tsanyawa, Sani Bala, ya ce rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 10 ne suka maƙale a ramin.

Ya buƙaci hukumomi su kawo agajin gaggawa tare da neman a turo da kayan aikin ceto na musamman domin kai ɗauki

“Muna buƙatar taimakon gaggawa domin ceto waɗanda suka maƙale. Al’umma na iya ƙoƙarinsu, amma ana buƙatar ƙwararrun masu aikin ceto,” in ji shi.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, an shafe sama da awa biyar ana ƙoƙarin ceto waɗanda suka maƙale.

Sai dai har yanzu ba a ceto mutane da dama ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankali, kuma ana hasashen adadin waɗanda suka rasu na iya ƙaruwa.

Mazauna yankin sun ce irin wannan iftila’i ba sabon abu ba ne a ƙauyuka, inda ma’aikata ke aiki a cikin ramuka masu zurfi ba tare da isassun matakan tsaro ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *