Kykkyawar Fata Ga Ziyarar Da Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Kai A Afirka

[ad_1]

Ranar Litinin 12 ga wannan wata na Janairu ne ministan kula da harkokin wajen kasar Sin, Mr. Wang Yi ya kammala ziyararsa zuwa nahiyar Afrika, inda ya ziyarci hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da kasashen Habasha, da Tanzania, da Lesotho. Wannan ziyarar diplomasiyya ta kasance ziyara ta farko a hukumance da Sin ta fara kaiwa a wannan sabuwar shekara ta 2026, kuma a nahiyar Afirka. Afirka dai na ci gaba da kasancewa nahiya ta farko da kasar Sin take fara kai ziyara a kowace sabuwar shekara a cikin shekaru 36 ke nan a jere. Shin ko mene ne sirrin na fara bude ziyararta da kasashen Afirka?

Ziyarar ta kwanaki biyar, wadda ministan harkokin wajen na Sin ya fara daga ranar Laraba 7 ga wannan wata na Janairu ya kammalata ne ranar Litinin 12 ga watan Janairu. Ya kuwa fara aiwatar da wannan ziyara a kasar Ethiopia, wato Habasha, hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka (AU), inda daga nan kuma ya zarce zuwa kasashen Tanzania da Lesotho. Wannan ziyara ta zuwa yankin gabashi da kudancin nahiyar Afirka yana da matukar mahimmaci, musamman ta fuskar bunkasa cinikayya tsakanin Sin da wadannan kasashe. Kazalika ziyarar ta kara zurfafa aminci tsakanin bangarorin biyu ta fuskar siyasa da zamantakewa.

Akwai nasarori da dama da wannan ziyarar Mr. Wang ta samu, musamman idan aka yi la’akari da cewa ziyarar ta zo daidai lokacin da ake bukatar hakan. Saboda baya ga kasancewar cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, wannan ziyara ta zo daidai da lokacin da wasu kasashen Afirka suka shiga cikin halin ni ’ya su ta fuskar tattalin arziki, sakamakon manufofin nan na rashin imani da Amerika ta bullo da su, kama daga batun tsauwala harajin cinikayya, tsananta matakan samar da visa da batun tursasawa wasu kasashen Afirka karbar bakin hauren da Amerika take son raba su da kasar.

Sabo da haka wannan ziyara ta samu nasarar kwantar da hankalin kasashen da suka fada cikin mawuyacin hali na tattalin arziki da rikicin siyasa sakamakon munanan manufofin Amerika da kasashen Turai kan kasashen Afirka. Abin da ya kara baiwa wadannan kasashe kwarin gwiwar cewa, kasar Sin tana tare da su ko wuya ko dadi, kuma a ko wane lokaci.

Alfanun hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a bayyane yake, musamman idan aka yi la’akari da irin dubban kilomita na layin dogo da titunan mota da kamfunnan Sin suka shimfida a kasashe daban daban na Afirka, abin sai san barka. Baya ga wannan kuma ga gadoji da tashoshin jiragen ruwa da filayen saukar jiragen sama masu dimbin yawa da kasar ta Sin ta samar a kasashen na Afirka.

Nasara a bangaren cinikayya kuwa, Sin ta kasance babbar kawar cinikayya da kasahen Afirka sama da shekaru 16. A bara, darajar cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta zarce dala biliyan 300. Sabo da yayin da Amerika take ta tsauwala harajin cinikayya kan kasashen Afirka, ita kuwa kasar ta Sin janye harajin cinikayyar ta yi kwata kwata ga kasashen Afirka dake da dangantakar diplomasiyya.

A dunkule, nasarorin da wannan ziyara da minstan harkokin wajen na Sin ya kai a Afirka sun hada da zurfafa dangantakar tattalin arziki, bunkasa harkokin cinikayya tsakanin Sin da Afirka da kuma inganta hadin gwiwa ta fannin kiwon lafiya, tsaro da kuma samar da ababen more rayuwa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *