’Yan sanda sun kama wata kan zubawa ɗan shekara 3 guba

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta cafke wata mata mai suna Nafisat Lateef da laifin kashe wani yaro ɗan shekara uku da guba a unguwar Omifon da ke ƙaramar hukumar Odigbo.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya bayyana kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce wanda aka kashe ɗin yaron ɗan gidan hayan matar ne.

A cewar Jimoh, wacce ake zargin mai shekara 40 ta aikata laifin ne a ranar Talata bayan gardama da mahaifiyar mamacin, mai suna Rofiat. An ruwaito wanda ake zargin ta bai wa yaron wani abu mai ruwa da ake zargin yana da guba.

Jimoh ya ce: “Al’amarin ya faru ne a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairun 2026, da misalin ƙarfe 8:30 na safe, inda ake zargin wacce ake zargin ta baiwa wanda aka kashe ɗin a matsayin Abdulrasheed, wani abu mai ruwa da ake zargin guba ne.

“An ruwaito cewa, an yi wannan aika-aikan ne biyo bayan rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin mai ƙorafin da wacce ake zargin, wanda ita ce mai gidan hayan mahaifiyar yaron .

“Ba da jimawa yaron ya shanye abin da ta ba shi, sai ya fara amai, nan take aka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, don samun kulawar likitoci.

“Jami’an ‘yan sanda, a yayin wani samame cikin gaggawa da jami’an leƙen asiri, suka kama wanda ake zargin.”

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun gano sinadarin da ake zargin guba ne a yayin binciken.

“A halin yanzu wanda ake zargin tana hannun ‘yan sanda kuma an gano bayanai masu amfani,” in ji Jimoh.

‘Yan sanda sun fara gudanar da cikakken bincike, kuma za a gurfanar da ita gaban kotu bayan kammala binciken.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *