Kasar Sin Na Da Kayayyakin Tarihi Na Halittu Na Duniya Guda 15
[ad_1]
Hukumar kula da sha’anin gandun daji da filin ciyayi ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru a yau Juma’a, inda aka kaddamar da rahoto game da kiyayewa da ci gaban kayayyakin tarihi na halittu na duniya a kasar Sin daga shekarar 1985 zuwa 2025.
Wannan ne karo na farko da rahoton ya kimanta kayayyakin tarihi na halittu na kasar Sin a dukkan fannoni, kuma sakamakon ya bayyana cewa, duk kayayyakin tarihi na halittu na kasar na kasancewa yadda ya kamata, ba a samu lalacewarsu mai tsanani daga hannun dan’Adam ba, ko kuma kawo tasiri mara kyau ga wuraren da kayayyakin suke ciki. Bisa kididdigar da aka yi an nuna cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin na da kayayyakin tarihi na halittu na duniya guda 15, kayayyakin tarihi da suka shafi hallitu da al’adu baki daya guda 4, adadin da ya kai matsayin farko a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link