Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 29 a Borno da Yobe

[ad_1]



Sojojin rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 29 a wasu jerin hare-haren da suka kai a jihohin Borno da Yobe tsakanin Asabar da Lahadi.

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an gudanar da ayyukan ne a ƙauyen Lamusheri da ke ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe, da kuma a sansanonin sojoji na Limankara da Kukawa a Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, jami’in yaɗa labarai na rundunar OPHK, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce hare-haren sun ƙara matsin lamba kan maɓoyar ’yan ta’addan a faɗin yankin Arewa maso Gabas.

“Dakarun Operation Haɗin Kai sun sake nuna ƙwarewa da jajircewa wajen daƙile hare-haren ta’addanci da aka shirya a Limankara da Kukawa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa sojoji sun kashe ’yan ta’adda 15 a Gujba, yayin da aka kashe 14 a Kukawa.

A cewar majiyoyin tsaro, an buɗe wa sojojin wuta waɗanda suke tare da wata rundunar farar hula yayin da suke matsowa kusa da wuraren da lamarin ya faru, amma sun yi nasarar fatattakar ’yan ta’addan.

Sojojin sun kuma gano tare da lalata wasu gine-gine da wuraren da ake amfani da su wajen gudanar da harkokin yau da kullum na ’yan ta’addan a yankunan.

Bugu da ƙari, an lalata babura guda biyar da motoci biyu da ake zargin ’yan ta’addan na amfani da su wajen kai hare-hare da jigilar kayayyaki.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da tarin makamai da harsasai, da kuma wasu jakunkuna na kayayyakin masarufi.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga a yayin aikin, amma suna ci gaba da murmurewa a ƙarƙashin kulawar mahukunta na lafiya.

Ta kuma jaddada cewa duk da an samu sauƙin matsalar tsaro gaba ɗaya a yankin, ana ci gaba da sa ido tare da ƙarfafa matakan tsaro, lamarin da ke ƙara wa sojojin ƙwarin gwiwar jajircewa wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *