Butulu ne ke son bata sunan Ali Nuhu-Papalaje
[ad_1]
Butulu ne ke son bata sunan Ali Nuhu-Papalaje
A farkon makon jiya ne shahararren marubucin littattafan Hausa da finafinan Hausa kuma Darakta a Kannywood, AbdulKarim Papalaje ya fito ya rubuta a kan shafinsa na Facebook yana maganganu na harbin iska da jankunne ga wani da ya kira mai son yi wa Shugaban Hukumar Fim ta Qasa Dakta Ali Nuhu rashin kunya da butulci da bata suna.
Papalaje a cikin rubutun ya yaba wa gudumawar da Ali ke bayarwa wajen ci gaban ayyukan da suka shafi harkokin shirya finafinan Kannywood ta haryar ba wa da dama daga cikin jarumai da daraktoci damar qaa ilimi don inganta sana’arsu.
Haka kuma ya ja kunnen masu son su vata wa Dakta Ali Nuhu suna, duk kuwa da yake kuwa masu yin hakan su suka fi kowa qaruwa da Alin. Sannan kuma a cewarsa, “Dakta Ali Nuhu yana bakin qoqarinsa wajen taimaka wa Kannywood.”
Koda a ‘yan makonnin baya ma dai an samu wani qorafi daga bakin wani jigo a Kannywood wanda ya yi zargin cewa, Hukumar Fim ta Qasa a qarqashin jagoracin Ali Nuhu ta dena damawa da su.
Rubutun Papalaje na bayan nan na nuna akwai alamun wasu jarumai da manyan Kannywood basu gamsu da yadda Ali Nuhu ke tuya yana son mantawa da albasa ba.
Haka kuma rubutun ya jawo zazzafar muhawara a kan shafin Facebook na Papalaje inda da dama waxanda suka tsoma baki suka yaba da yadda Dakta Ali Nuhu ke gudanar da ayyukan Hukumar Fim ta Qasa.
[ad_2]
Source link