Tsaro: Sojoji Sun Gano Masana’antar Ƙera Makamai A Nasarawa

[ad_1]

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce Sojojinta na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun “gano wata masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba a ɓoye a yankin Agwatashi da ke ƙaramar hukumar Doma a Jihar Nasarawa.”

Sojojin sun gano wurin ne yayin da suke gudanar da aikinsu na sintiri domin hana masu aikata laifuka yin kutse da samun ‘yancin motsi.

  • Gwamna Lawal Ya Fara Ganawa Da Manyan Jiga-jigan PDP A Zamfara
  • Da Gaske Ne Babu Tashar Samar Da Lantarki Ta Karfin Iska A Kasar Sin?

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.

Rahotanni sun nuna cewa wurin an ɓoye shi ne domin ƙera makaman da ake bai wa masu aikata laifuka a yankin da ma wajen sa.

Da isar sojojin wurin, wasu mutane da ake zargi sun tsere amma daga baya aka kama mutum ɗaya ɗan shekara 26 daga ƙauyen Arusu a ƙaramar hukumar Kokona, yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta hanyar ɓoye kansa a kan wata bishiya.

Binciken da aka yi a wurin ya kai ga gano bindigogi guda shida da aka ƙera da kayan aiki da na’urorin da ake amfani da su wajen ƙera makamai da kuɗi da kuma wayar salula da aka samu a hannun wanda aka kama.

Binciken farko ya nuna cewa “wurin na samar da makamai ga ‘yan ta’adda a ciki da wajen yankin.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *