Yadda sabbin dokokin haraji za su shafi ’yan Najeriya a 2026

[ad_1]



Kamar yadda aka tsara a yau 1 ga watan Janairun 2026, sabbin dokokin harajin da Shugaba Bola Tinubu, ya sanya wa hannu za su fara aiki.

An kai ruwa rana kan fara aiwatar da dokokin, inda aka yi tunanin za a dakatar da su saboda wasu zargin yi musu cushe, lamarin da ya bambanta su da na asalin da Majalisar Dokoki ta amince da su.

Sai dai, a ranar 30 ga watan Disamban 2025, Shugaba Tinubu, ya ce ba gudu ba ja da baya kan aiwatar da harajin domin hakan zai hana Najeriya cimma burinta na bunƙasa tattalin arziƙinta.

Ya ƙara da cewa yana sane da zarge-zargen da ake yi kuma yana aiki tare da Majalisun Tarayya don nemo mafita.

Ta yaya sabon harajin zai shafi ’yan Najeriya?

Wane ne zai biya harajin?

Duk wani ɗan ƙasa da ke samun kuɗin shiga a Najeriya kama daga kan ma’aikaci, ɗan kasuwa, mai shirye-shirye a kafafen sada zumunta, ko kamfani, zai biya haraji.

Haka kuma duk wanda ke samun kuɗi daga ƙasashen waje amma yana zaune a Najeriya, shi ma sai ya biya haraji.

Sai dai akwai sassauci: Duk wanda kuɗin shigarsa bai wuce Naira 800,000 a shekara ba, ba zai biya harajin kuɗin shiga ba.

Wannan yana nufin ma’aikatan da ke karɓar mafi ƙarancin albashi ba za su biya ba.

Nawa ne harajin?

Hukumar Tattara Haraji ta Najeriya (NRS) ta bayyana cewa yawan kuɗin da mutum ke samu shi ne zai tantance adadin da zai biya:

  • Babu haraji kan N800,000 da mutum ya samu
  • Daga N2,200,000 – kaso 15
  • Daga N9,000,000 – kaso 18
  • Daga N13,000,000 – kaso 21
  • Beraye N25,000,000 – harka 23
  • Beraye N50,000,000 – case 25

Abubuwan da ba za a biya musu haraji ba

  • Kuɗin da mutum ke samu kamar mafi ƙarancin albashi
  • Kuɗin fansho, garatuti, inshora, lamunin gida
  • Kuɗin da aka samu daga siyar da motoci da gidaje, da wasu ƙananun kadarori
  • Kyaututtuka da kuɗaɗen ayyukan jin-ƙai
  • Masana’antu da ƙananan kasuwanci da ribarsu ba ta wuce N100,000,000 ba
  • Harajin VAT a kan kayan abinci, haya, lafiya, magunguna, kayan noma da sauransu

Ta yaya za a cire harajin?

1. Harajin ma’aikata (PAYE):

Za ake cire harajin kai-tsaye daga albashin ma’aikata a kowane wata. Wannan yana kama da tsarin cire kuɗin fansho ko lamunin gida.

2. Harajin ’yan kasuwa:

Za ake biyan harajin ne a ƙarshen shekara bisa ribar da ɗan kasuwa ya samu. Bankuna za su sanar da hukumar haraji idan hada-hadar wani kamfani ko mutum ya kai Naira miliyan 25 ko Naira miliyan 50 a watanni uku.

Bankuna za su cire haraji daga asusun mutane?

Bankuna ba za su taɓa cire haraji daga asusun mutum kai-tsaye ba. Abin da za su yi shi ne sanar da hukumar haraji idan an samu hada-hadar kuɗi mai yawa a asusun mutum.

Waɗanda aka yi wa sassauci wajen biyan harajin

Ma’aikaci da albashinsa bai wuce Naira miliyan 20 a shekara ba, zai biya kaso 18 maimakon 25 da ake biya a baya.

Masu biyan kuɗin haya za su samu ragin kaso 20.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *