An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa

[ad_1]

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Mustapha Ismail, mai shekara 25, bisa zargin kashe abokinsa, Halifa Tijjani, bayan rigima ta kaure a tsakaninsu.

Kakakin rundunar jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Disamba, 2025 bayan samun saɓani a tsakaninsu.

  • Shugabannin Sin Da Rasha Sun Yi Musayar Gaisuwar Sabuwar Shekara
  • Peter Obi Da Shugabannin Kudu Maso Gabas Sun Koma Jam’iyyar ADC A Enugu

‘Yansanda sun ce rigimar ta rikide zuwa faɗa, inda ake zargin Mustapha ya soki Halifa, mai shekara 24, da wuƙa a baya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

SP Kiyawa, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma a halin yanzu jami’an tsaro na bincike a kansa a Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Bompai.

A yayin gudanar da bincike, Mustapha ya ce yana shan miyagun ƙwayoyi, kuma ya bayyana cewa rigimar ta fara ne yayin da suke kallon bidiyo a wayarsa.

Ya ce ya gargaɗi Halifa kada ya lalata masa waya, amma ya ƙi ji.

Daga nan suka fara zagin juna, lamarin da ya rikiɗe zuwa faɗa.

Ya ce Halifa ne ya fara sokukarsa da wuƙa, shi ma daga baya ya soke shi a baya.

‘Yansanda sun ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *