Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio

[ad_1]



Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya.

Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zabe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba.

“Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin harkar siyasa, na san ba mu damu da jam’iyya ba, ana iya lashe zabe a ko’ina.

“Ka na da ƙwarewa sosai, amma za ka yarda da ni cewa tun bayan faduwar PDP, zabe ya inganta matuka a wannan ƙasa.

“Na tuna, ina da kusanci da yawancin shugabannin ƙasa tun daga 1999, kuma a 2007 lokacin da na ci zabe a matsayin gwamna, shugaban ƙasa na lokacin, Allah ya jiƙansa, Shugaba Yar’Adua, ya fito fili ya ce zaben da ya kawo shi mulki yana da lam’a.

“Ya ce cike yake da kura-kurai da magudi. Tun daga lokacin, muka fara rufe guraben da ke haifar da matsala.”

Akpabio ya ƙara da cewa duk da cewa ’yan Najeriya na fuskantar ƙalubale, tsarin ya inganta.

“Ka duba zaben da ya gabata, har sai da muka je Kotun Koli muna muhawara kan ko lashe babban birnin tarayya kadai ya isa ya sa dan takara ya zama shugaban ƙasa,” in ji shi.

“Hankali kawai ya isa ya gaya mana cewa ba haka dokar zabe take nufi ba,” in ji Akpabio.

Shugaban majalisar dattawa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki bayan PDP ta fadi zabe a shekarar 2015.

Ya tsaya takarar Sanata a 2019 a karkashin jam’iyyar APC, amma bai ci ba.

Sai dai tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi minista daga bisani, kafin a 2023 kuma ya ci zaben sanatan daga jiharsa ta Akwa Ibom, sannan aka zabe shi shugabancin majalisar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *