Jagoran ’yan bindiga a Taraba da Binuwai ya shiga hannun sojoji

[ad_1]



Sojojin sun kama wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da ya daɗe yana addabar al’ummomi da matafiya a kan hanyar Binuwai zuwa Taraba.

A ranar Lahadi 21 ga Disamba, 2025 sojoji a ƙauyen Vaase da ke Ƙaramar Hukumar Ukum da ke Jihar Benue, bayan samun sahihin bayanan sirri.

Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana a Jalingo cewa sojojin sun kama Fidelis Gayama, wanda ya kasance cikin jerin mutanen da hukumomin tsaro ke nema a yankin Taraba da Binuwai.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama na da alaƙa ta kusa da Aka Dogo, wani shugaban ƙungiyar ’yan ta’adda da ake nema, kuma ana zargin shi ne jagoran wata ƙungiyar masu aikata laifuka da suka addabi matafiya da al’ummomi a kan hanyar Kente–Wukari da kuma yankunan iyaka na Binuwai da Taraba.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa wanda aka kama yana hannun sojoji a halin yanzu, kuma za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin gudanar da cikakken bincike da gurfanar da shi a kotu.

A yayin da yake yabawa sojojin bisa ƙwarewa wajen gudanar da aikin, kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya ta Biyu / Sector 3 OPWS, Brigediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya bayyana wannan kamen a matsayin babban cikas ga cibiyoyin laifuka da ke aiki a yankin.

Ya kuma jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *