Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sake jaddada haramcin hawa babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe, a wani mataki na tsaurara tsaro yayin bikin Mauludi a jihar.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa dokar na da muhimmanci domin hana aikata laifuka musamman a lokutan bukukuwa.

Ya ce an baza jami’an tsaro a wuraren taro, wuraren Mauludi da sauran wurare.

Kwamishinan ya gargaɗi jama’a da cewa dokar hana ɗaukar makamai tana nan daram, kuma duk wanda aka kama da su zai fuskanci hukunci.

Ya kuma ce ba za a lamunci tashin hankali ko karya doka ba.

Haka kuma rundunar ta roƙi shugabannin addini, masu shirya bukukuwa da sauran masu ruwa da tsaki da su kula da mabiyansu tare da yin aiki tare da jami’an tsaro.

Ta kuma buƙaci jama’a da su kai rahoton duk wani abu ko mutum da suke zargi, tare da gujewa duk wani abu da zai iya haifar da rikici.

Sannan rundunar ta yi fatan Musulmi za su gudanar da bikin Mauludi cikin kwanciyar hankali.

Hakazalika, ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *