Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 3, sun ceto mutum 3 a Gombe
[ad_1]
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga uku tare da ceto wasu mutum uku da aka sace a wani hari da aka kai yankin Pindiga–Kashere a Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.
Harin ya faru ne a ƙauyukan Rahama, Lambo da Garin Galadima a gundumar Pindiga da sanyin safiyar ranar Juma’a, 24 ga watan Janairu, 2026.
Wannan ma cikin sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun fara kai farmaki ƙauyen Rahama da misalin ƙarfe 2 na dare ta hanyar Gagarabami, inda suka kashe wani dattijo mai shekaru 70 mai suna Tela Bello Ahmadu.
Bayan haka, sun sace ’ya’yansa biyu, Saleh Tela (25) da Abdullahi Tela (35).
Daga nan kuma, maharan suka wuce ƙauyen Lambo ta hanyar Pindiga–Kashere inda suka sace Babayo Garba (30), Malam Abba Musa (45) da Baayo Bayi (20).
Bayan samun rahoton faruwar harin, jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Hattara tare da haɗin gwiwar mafarauta da ’yan sa-kai suka nufi dajin da ’yan bindigar suka tsere, inda aka yi artabu.
A yayin artabun, Baayo Bayi ya samu rauni kafin daga baya ya rasu, yayin da aka ceto Babayo Garba da Malam Abba Musa.
Jami’an tsaron sun kuma kashe ’yan bindiga uku, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji.
An ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, majigi huɗu, harsashi 68, da ƙunshin harsashi 120, babura huɗu da kuma kuɗi Naira Naira 2,300.
An kai waɗanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsu, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da farautar sauran ’yan bindigar da suka tsere.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Pindiga–Kashere da sauran sassan jihar.
Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link