APC Ta Musanta Bai Wa Gwamnonin Da Suka Sauya Sheƙa Tikitin Takara Na Kai Tsaye A 2027
[ad_1]
Manyan shugabannin jam’iyyar APC sun yi watsi da bayar da tikitin kai tsaye ga gwamnonin jihohi da suka sauya sheƙa, ciki har da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, waɗanda suka shiga jam’iyyar kwanan nan, haka kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ake sa ran zai shiga nan ba da jimawa ba.
Wani mamba na kwamitin gudanarwa na APC, wanda ya yi magana ba tare da ya bayyana sunansa ba saboda bai samu izinin yin tsokaci kan batun ba, ya bayyana cewa komawa daga wata jam’iyyar siyasa zuwa APC ba ya tabbatar da samun tikitin kai tsaye.
- Bayan Ganawa Da Tinubu, Gwamna Abba Zai Iya Komawa APC A Talata Ko Laraba
- Tinubu Ya Saita Wa Gwamna Yusuf Hanyar Sauya Sheƙa Zuwa APC
A bisa goyon bayan wannan matsayi, Daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, a wata hira ta musamman da manema labarai, ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da dimokuraɗiyya da ci gaba, yana jaddada cewa za a ba dukkan mambobi damar yin takara ba tare da hana wasu ba.
Daga cikin gwamnonin PDP da suka koma APC akwai Umo Eno na Jihar Akwa Ibom da Sheriff Oborevwori na Jihar Delta da Peter Mbah na Jihar Inugu da Agbu Kefas na Jihar Taraba da kuma Siminalayi Fubara na Jihar Ribas.
Shugabancin APC a Jihar Kano sun nuna cewa sauya sheƙar gwamnan jihar na gab da faruwa.
Bayan gwamnonin, wasu fitattun ‘yan siyasa da dama ciki har da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da kuma tsoffin gwamnonin da tsoffin ministoci da sauran shugabannin jam’iyya suma sun bar PDP zuwa APC.
Ko da yake masu sauya sheƙar sun bayar da dalilai daban-daban na shiga jam’iyyar mulki, wasu ‘yan Nijeriya na cewa gaskiyar dalilin shi ne samun sake zaven su zuwa muƙaman da suke kai.
A cikin martaninsa, wani mamba na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ya ce canje-canjen sun samo asali ne daga nasarorin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ya ce a ƙarshe dai mutane ne za su yanke hukunci na sake zavensa.
[ad_2]
Source link