Kasar Sin Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Hana Japan Sake Rungumar Ra’ayin Amfani Da Karfin Soji

[ad_1]

Babban jami’in kasar Sin a ofishinta dake MDD Sun Lei ya bukaci kasashen duniya da su hada hannu wajen kare nasarorin da aka cimma a yakin duniya na biyu, ciki had da hukuncin da kotun soja ta Gabas mai nisa ta yanke kan masu aikata miyagun laifuffukan yaki na Japan, a kokarin hana Japan sake rungumar ra’ayin amfani da karfin soji da ta taba yi a baya.

Sun ya bayana haka ne jiya Litinin 19 ga wata a yayin taron farko da kwamitin shirya taron MDD na hanawa da hukunta masu aikata laifuffukan illata bil’Adama.

A wannan rana kuma, yayin da ake nazarin batun kotun hukunta munanan laifuffuka ta kasa da kasa dangane da Sudan, Sun Lei ya jaddada cewa, kamata ya yi kotun hukunta munanan laifuffuka ta kasa da kasa ta kauce wa siyasantar da wasu batutuwan duniya da na shiyya-shiyya masu jawo hankali, ta kuma yi watsi da nuna fuska biyu. Sun Lei ya ci gaba da cewa, wajibi ne kotun hukunta munanan laifuffuka ta kasa da kasa ta mutunta ikon Sudan na aiwatar da doka da tafiyar da harkokinta da kanta, ta saurari kulawar gwamnatin Sudan, a kokarin kashe wuta. Kana, wajibi ne kotun ta goyi bayan Sudan ta inganta tsarin kasar na aiwatar da doka da kyautata kwarewa, ta yadda za ta kara tabbatar da gaskiya da adalci. (Tasallah Yuan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *