Za A Yi Jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi A Gobe Juma’a

[ad_1]


An ware ranar gobe Juma’a domin yin jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Kofar Gombe a cikin garin Bauchi.

Fitaccen Malamin wanda ya yi fama da jinya ya kasance wanda ya bayar da gudummawa sosai wajen ci gaban addinin Musulunci a Nijeriya da ma Afrika.

An haifi Sheikh Dahiru Usman ne a ranar 2 ga Almuharram 1346 A.H a garin Nafada da ke jihar Bauchi a wancan lokacin (yanzu ta na jihar Gombe).

Jagora a Ɗarikar Tijjaniyya ya bar duniya da mata huɗu, ‘ya’ya sama da ɗari da jikoki da sama da 400, da tattaɓa kunne 100.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa Sheikh Dahiru ya fara Tasirin Alkur’ani ne a Bauchi tun 1948. Ya kasance mai gudanarwar da tafsirin watan Ramadana a jihohin Bauchi da Kaduna.

Kafin rasuwarsa shi ne mataimakin shugaban kwamitin Fatwa na Majalisar koli ta addinin Muslunci (Supreme Council of Islamic Affairs.)

Hadiminsa M Daha Azhary Bauchi shi ne ya sanar da cewa za a yi jana’izar ne a ranar Juma’a

Ya ce, “Za a yi Sallar Jana’izar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gobe Juma’a 28-11-2025 a Bauchi.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *