Abin da sauya sheƙar Abba zai haifar a siyasar Kano

[ad_1]



Shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC ya jefa tafiyar Kwankwasiyya, wadda uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yake jagoranta, cikin rudani.

Majiyoyi da dama sun ce, babu gudu, babu ja da baya kan hukuncin da gwamnan ya yanke, ko da kuwa hakan zai kawo cikas tsakaninsa da Kwankwaso.

Sanata Kwankwaso shi ne wanda ya kafa tafiyar Kwankwasiyya kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Abba a zaben gwamna a 2023.

Sauya sheƙar Abba da ke tafe ta sake tayar da tsoffin taƙaddama a siyasar Kano, da kuma tambayoyi kan makomar tafiyar Kwankwasiyya, tare da sake fasalin lissafin siyasar jihar gabanin zaɓen 2027.

Wasu masu kusanci da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun ce ya yanke wannan hukunci ne bayan shawarwari da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ’yan majalisar tarayya daga jihar.

Wani babban hadimin gwamnan, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce rikicin cikin gida a NNPP ce kan gaba wajen sanya gwamnan ya ɗauki wannan mataki, domin a cewarsa, rikicin na barazana ga damarsa ta neman wa’adi na biyu.

“Babban dalili shi ne NNPP ta zama ba ta da ƙarfi saboda shari’o’i da yawa da ake yi a kanta,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ko da gwamnan ya ci gaba da zama a NNPP, ’yan kanzagin Kwankwaso sun riga sun yanke hukunci cewa ba za su ba shi tikitin takara ba, suna shirin bai wa mataimakin gwamna damar tsayawa.

Majiyar ta ce adawar da ake yi wa Gwamna Abba ta samo asali ne daga tsoron cewa ayyukansa da shaharar da yake samu a faɗin jihar na iya disashe tasirin Kwankwaso.

“Ba sa son ya fi Kwankwaso haske. Ayyukansa a bayyane suke, kuma ba sa son ya ci gaba,” in ji shi.

Game da dangantakar Abba da uban gidan siyasarsa, hadimin ya ce aikin gama ya riga ya gama, “Kwankwaso ba ya son wannan gwamna ya dawo. Sabon mutum yake so. Idan APC ta ba shi damar sauya gwamna, zai amince.”

Majiyar ta musanta jita-jitar cewa an tsara ranar sauya sheƙar, inda ta ce hakan na iya faruwa a kowane lokaci. “Ba a tsayar da rana ba. Duk ranar da kuka ji, jita-jita ce. Amma dai, zai faru,” in ji ta.

Da aka tambaye ta ko akwai yiwuwar sulhu, sai ta ce, “To Wa zai shiga tsakani? Waɗanda ya kamata su sasanta sun riga sun ɗauki ɓangare. Kowa ya riga ya yanke hukunci.”

Kwankwasiyya ta rabu gida biyu

Rahotanni sun nuna cewa wannan lamarin ya raba tafiyar Kwankwasiyya zuwa ɓangarori biyu.

Bangaren farko yana goyon bayan Kwankwaso, kuma ya haɗa da mataimakin gwamna, sanata daya tilo na jam’iyyar, kwamishinoni biyu (na kasuwanci da na kimiyya da fasaha), mai ba da shawara na siyasa ga gwamna da kuma shugaban jam’iyyar NNPP na jihar.

A daya ɓangaren kuma akwai Gwamna Abba, da ’yan majalisar wakilai 13, da kwamishinoni 23, shugaban majalisar dokokin jihar, da ’yan majalisa jiha 19 da dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44.

Wannan bangare ana ganin Shugaban Majalisa, Shugaban ALGON da daraktan fadar gwamna na al’amuran gudanarwa ne ke jagorantar sa.

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Kano, Rt Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya tabbatar da ganawarsa da Gwamna Abba a ranar Lahadi, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan shirin sauya sheƙar gwamnan.

Rurum, wanda yanzu ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Rano/Bunkure/Kibiya a Majalisar Tarayya ne, kuma ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC kwanan nan, ya c ba su tattauna batun Kwankwaso a cikin wannan ganawa ba.

“A tsawon tattaunawar ba mu yi maganar Kwankwaso ba. Mun yi gamana ne a kan wasu muhimman batutuwa game da sauya shekara Gwamna, amma ba mu yi maganar tafiyar Kwankwaso ba,” in ji shi.

Wasu masu ruwa da tsaki sun shaida wa wakilinmu cewa Kwankwaso ya gudanar da tarob sirri da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar Litinin a wani ƙoƙarin ƙarshe da nufin dakatar da sauya shekar, yayin da ’yan majalisar da ke goyon bayan Gwamna Abba suka shirya ganawa da gwamnan domin bayyana goyon bayansu.

Wata majiya da Kwankwaso ta ce, “Kwankwaso ya shiga damuwa sosai kuma a farko bai yarda cewa Abba zai yi masa tawaye a fili ba, Daga dukkan tarurrukan da aka yi, ya bayyana cewa sauya shekar ya kammala. Abin da ake fata kawai shi ne gwamnan ya sake tunani.”

Rikicin tun kafin sauya sheka

Majiyoyi sun ce rashin jituwa tsakanin Abba da Kwankaso ya fara ne tun kafin Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki.

An ce Kwankwaso ya nuna sha’awar tattaunawa da APC domin samun mukami a gwamnatin tarayya, amma tattaunawar ta rushe bayan fadar shugaban ƙasa ta lura cewa bukatunsa sun yi da kuma barazanar ƙarfafa matsayinsa a Arewa wajen neman mulki a 2031.

Bayan rushewar tattaunawar, shugabannin APC suka karkata ga Gwamna Abba ta hanyar Kungiyar Gwamnonin APC, abin da ya fusata Kwankwaso.

Wata majiya ta ce a dalilin haka ne Kwankwaso “Yana ganin kamar an raina shi saboda tattaunawar ta ci gaba ba tare da shi ba.”

Wannan sabani ya kuma taka rawa wajen korar Abdulmumin Jibrin Kofa daga NNPP, bayan Kwankwaso ya zarge shi da yin magana da Tinubu kai tsaye a maimakonsa.

Wata majiya ta ce APC ta fi samun sauƙi wajen tattaunawa da Abba. “Abin da gwamnan yake so shi ne tabbacin wa’adin mulki na biyu. Amma Kwankwaso yana son ikon jam’iyya, muƙaman gwamnatin tarayya ƙasa da tasiri a Kano da Arewa maso Yamma. Wannan ya yi yawa,” in ji majiyar.

Shugabannin NNPP sun juya baya

Shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashim Suleiman Dungurawa, ya yi watsi da shirin sauya sheƙar, inda ya roƙi mambobi “don Allah da Manzon Allah” kada su bar jam’iyyar.

Dungurawa ya musanta zargin cewa shugabannin jam’iyya suna ƙoƙarin haddasa sabani tsakaninsu da Kwankwaso, sai dai masu sharhi sun ce adawarsa na iya zama saboda tsoron rasa tasiri idan Gwamna Abba ya tafi da majalisar zartarwa.

Sanata ɗaya tilo na NNPP, Rufa’i Sani Hanga, ya yi watsi da batun sauya shekar a matsayin ƙirƙira, yana gargadin cewa “’yan Kano ba sa goyon bayan masu cin amana.”

Ra’ayoyi mabambanta

Ɗan gwagwarmayar Kwankwasiyya, Kwamre Sule Ya’u Tariwa, ya yi gargadin cewa rashin jituwa na iya tarwatsa tafiyar, a yayin da ɗan jarida Jaafar Jaafar ya tuna da tallafin kuɗi da Kwankwaso ya taɓa yi wa Abba a baya.

Wasu sun kafa hujja da cewa Kwankwaso zai iya rasa tasiri idan ya koma APC, amma zai iya kare matsayinsa da abin da ya kafa ta hanyar kiyaye NNPP.

Wasu kuma sun yi maraba da sauya sheƙar. Tsohon minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya bayyana matakin a matsayin “na kan gaba,” yana mai cewa daidaita Kano da Agaendar Gwamnatin Tinubu zai jawo tallafin tarayya ga jihar.

Amma jigo a APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya yi watsi da sauya sheƙar a matsayin makirci na tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje, domin hana Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin samun takarar gwamna a zaben 2027.

Sharhin masana

Masani kan siyasa a Kano, Kabiru Sa’idu Sufi, ya ce sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya lissafin siyasa a jihar.

“Mulkin gwamna yana da nauyi, amma zai haifar da rashin jin daɗi,” in ji shi, yana gargadin cewa NNPP za ta raunana kuma Kwankwasiyya ta rabu gida biyu.

An taɓa danganta Gwamna Abba Kabir Yusuf da APC a baya. Tun bayan hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da nasararsa, ake cewa ya riƙa ƙarfafa Kwankwaso ya shiga jam’iyyar mai mulki.

Gugugwar da ta taso a bara da taken “Abba Tsaya da Kafarka”, ta nuna kira da neman ’yancin kai, duk da cewa gwamnan ya jaddada biyayyarsa ga Kwankwaso a lokacin.

Sufi ya ce, a matsayin Kano na jiha mai mafi yawan al’umma a Najeriya, tana muhimmanci a siyasar ƙasa, kuma sauya shekar Abba na iya ƙarfafa lissafin zaben APC kafin 2027, sai dai kuma matakin ya ƙara tsananta rikice-rikicen cikin gida.

Ga NNPP, rasa gwamna ɗaya tilo na iya rage karfin jam’iyyar zuwa dandalin mutum ɗaya. Ga Kwankwasiyya kuma, wannan mataki na gwada ko tafiyar za ta iya dorewa ba tare da mulki ba.

Daga Sagir Kano Saleh, Clement A. Oloyede (Abuja), Yusha’u A. Ibrahim, Salim U. Ibrahim & Sani I. Paki (Kano)


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *