’Yan sanda sun ceto yaron da aka sace, sun kama mutum 5 a Borno
[ad_1]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno, ta samu nasarar ceto wani yaro ɗan shekara bakwai da aka yi garkuwa da shi a birnin Maiduguri, inda kuma ta cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta kuma ƙwato kuɗin fansar da aka biya.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, 2026.
Ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Naziru Abdulmajid.
A cewar rundunar, an shigar da rahoton sace yaron ne a ranar Talata, 24 ga watan Maris, da misalin ƙarfe 3:30 na rana, bayan da aka yi awon gaba da shi cikin dare a yankin ofishin Hukumar Tafkin Chadi da ke Maiduguri.
Masu garkuwar sun tuntuɓi mahaifiyar yaron ta waya, inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin fansa.
Daga baya, sun rage kuɗin zuwa Naira miliyan takwas, inda daga ƙarshe aka biya su Naira miliyan 1.5 ta hanyar amfani da POS.
Sakamakon bincike na ƙwaƙwaf, ’yan sanda sun bi sahun asusun da aka tura kuɗin, wanda hakan ya kai ga kama wani mai sana’ar POS mai suna Musa Mohammed Bashir.
Ta hanyar bincike aka damƙe wasu mutum huɗu a wasu wurare, ciki har da yankin Chad Basin da kuma Bulabulin Alajiri a cikin birnin na Maiduguri.
Rundunar ta tabbatar da cewa ta ceto yaron lami-lafiya, kuma bayan an duba lafiyarsa a asibiti, an miƙa shi ga iyayensa.
Haka kuma, jami’an sun yi nasarar ƙwato ɗaukacin Naira miliyan 1.5 da aka biya a matsayin fansa.
Kwamishinan ’Yan sandan jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da aikin saboda bajintar da suka nuna wajen gaggauta ceto yaron.
Ya kuma nanata ƙudirin rundunar na ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka, tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri a kan lokaci domin daƙile miyagun ayyuka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link