’Yan bindiga sun kashe manomi da sace wasu biyu a Sakkwato
[ad_1]
A wani sabon hari da ’Yan bindiga da suka kaiwa manoma sun kashe mutum guda sannan suka yi garkuwa da wasu mutane biyu a yankin Fadamar Kurawa da ke ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Wani ganau wanda ya tsallake rijiya da baya kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun farwa yankin ne a daidai lokacin da mazauna garin suke tsaka da girbin dankalin hausa a gonakansu.
A cewarsa, maharan sun isa gonakin ne da misalin karfe 10:30 na safe a ranar Alhamis, ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, inda suka buɗe wuta tare da tilastawa mutane tserewa.
Ya ce, “Sun zo sun tarar da yawancinmu a gonakinmu muna girbin dankali, sai suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa, wanda hakan ya sa manoma suka gudun ceton ransu.”
Ya ƙara da cewa, “Bayan sun fatattaki manoman, daga baya suka yi garkuwa da mutane uku, amma daga baya suka kashe ɗaya daga cikinsu saboda ya ƙi bin su zuwa maɓoyarsu.”
An bayyana sunayen mutane biyu da aka sace kamar haka: Idi Nana da kuma wata matar aure wadda aka sakaya sunanta.
Wata majiyar kuma ta ce ‘yan bindigar sun kai wa manoman harin ne a kan babura kusan guda shida, inda kowane babur yake ɗauke da mutane uku ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47.
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen ganin an ceto waɗanda aka sace, sannan a inganta tsaro a yankin baki ɗaya.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce ba su da labarin harin, amma ya yi alkawarin zai tuntubi wakilinmu bayan ya tantance lamarin daga jami’in ɗan sanda (DPO) na ƙaramar Hukumar Sabon Birni.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Rufa’i bai bayar da wani ƙarin bayani ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link