Kasar Sin: Ya Kamata A Karfafa Wa Amurka Da Iran Gwiwar Komawa Teburin Sulhu
[ad_1]
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya ce, Amurka da Iran na da sha’awar komawa teburin sulhu, kuma ya kamata kasashen duniya su karfafa musu gwiwar yin hakan, domin samar da ingantattun hanyoyin warware rikicin a siyasance.
Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne jiya Alhamis, yayin zantawar da ya yi da takwararsa ta Canada Anita Anand ta wayar tarho, bisa bukatar bangaren Canada.
A nata bangare, Anita Ananda ta bayyana wa Wang Yi matsayin da kasarta ta dauka kan batun Gabas ta Tsakiya. Tana cewa, burin Canada shi ne kare fararen hula a rikicin da yayyafawa yanayin ruwan sanyi da kare rikicin daga bazuwa da kuma rage tasirinsa kan tattalin arzikin duniya da tsarin ayyukan masana’antu da na samar da kayayyaki.
Ta kara da cewa, a shirye Canada take ta hada hannu da Sin wajen ingiza tsagaita bude wuta da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Bugu da kari, Wang Yi ya kara yin bayani game da matsayar Sin yana cewa, ya kamata a warware batun nukiliyar Iran ta hanyar tattaunawa, kuma bai kamata ya zama dalilin amfani da karfi ba. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)
[ad_2]
Source link