Gwamnonin Arewa Sun Goyi Bayan Tinubu, Sun Yi Alƙawarin Yin Aiki Tare Don Shawo Kan Matsalar Tsaro

[ad_1]

Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun sake jaddada goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu wajen yaƙar rashin tsaro da kuma bunƙasa ci gaban yankin.

Gwamnonin sun yi taro a Abuja, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

  • Atiku Ya Yi Wa Kwankwaso Maraba Da Zuwa ADC
  • Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan Kano, Nasiru Gawuna Ya Fice Daga APC

Bayan taron, sun yi alƙawarin ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin inganta tsaro.

Sun ce haɗin gwiwar da suke yi ya fara kawo sakamako mai kyau, tare da kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro baya.

Gwamnonin sun kuma amince da yin gyare-gyare a tsarin aikinsu, ciki har da amfani da fasahar zamani domin inganta aiki da haɗin kai.

A ɓangaren tattalin arziƙi, sun shirya nemo sababbin hanyoyin ƙara kuɗaɗen shiga ta hanyar gano hanyoyin haraji da ba a amfani da su sosai.

Haka kuma, sun nuna goyon baya ga ayyukan samar da makamashi, ciki har da shirin kafa kamfanin New Nigeria Energy Company.

Duk da haka, rashin tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale a yankin, inda hare-hare a jihohin Kaduna da Filato suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, raunata wasu, tare da raba wasu da muhallansu.

Gwamnonin sun ce za su ci gaba da haɗa kai da juna da kuma Gwamnatin Tarayya domin magance waɗannan matsaloli.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *