Shugaba Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Dandalin Kasuwancin Makamashi Na Sin Da Rasha
[ad_1]
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako taya murnar bude dandalin kasuwancin makamashi na Sin da Rasha karo na bakwai, wanda aka bude a nan birnin Beijing.
Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce Sin da Rasha sun fara aiwatar da hadin gwiwa a fannin makamashi tun da wuri, sun kuma kafa ginshiki mai karfi a fannin, matakin da ya kasance misali na tsarin cimma moriyar hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, wanda kuma ke taka muhimmiyar rawa ga bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar al’ummunsu da ma kyautata jin dadinsu.
Shi ma a nasa bangare, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya aike da sakon taya murnar bude dandalin. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link