Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa, ya ce zai kare kansa a kotu

[ad_1]



Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa.

A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba.

Lauyoyin da ke kare shi ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun yanke hukuncin cire hannunsu daga kare shi kan shari’ar da yake fuskanta.

Daga nan sai Kanu ya fara magana kai-tsaye, inda ya ƙalubalanci ikon kotu na ci gaba da yin shari’arsa.

Cikakken bayani zai biyo baya…


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *