SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari
[ad_1]
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka.
Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar.
Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu.
Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin biyan albashin watanni biyu da suke bi, da kuma jinkirin sabunta yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2009.
Haka kuma sun koka kan ƙin biyan kuɗaɗen da aka cire musu daga albashin watan Mayu da Yunin 2022.
Ƙungiyoyin sun ce wannan zanga-zanga na nufin tunatar da gwamnati muhimmancin mutunta yarjejeniyar da suka yi da kuma tabbatar da adalci ga ma’aikatan jami’o’i, domin ci gaban ilimi a Najeriya.
A gefe guda kuma, wa’adin da ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa kafin ta tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link